Danyen mai yayi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya, lalitarku zata ji qyaran
- Man ya tashi ne saboda taron OPEC
- Wannan na nufin Najeriya zata tara kudi daga rarar man
- Kasar nan ta dogara ne da man fetur
Danyen mai da Najeriya ke tatsa daga kudancin kasar nan, don moriyar kowa da kowa a fadin kasar nan, ya kara tashi, inda zai kai kusan dala 80 ko ma 90 idan dai ya ci gaba a haka a kasuwannin duniya kan kowacce garwa.
A yanzu dai ana sayar da man ne a dala 76 zuwa da takwas, inda yayi hobbasa daga 72-3 da yayi kan kowacce ganga a farkon shekarar nan.
Hadakar kasashen OPEC, watau masu sayar da mai, sun gama taron su inda suka cimma matsaya ta a rage fitar da man don farashinsa ya dan daidaita.
DUBA WANNAN: Hukuncin kisa ga shaihun Malami a wata kasa
Najeriya dai, bata fiye son ace mata ta rage fidda mai ba, saboda da shi ne ta dogara, musamman la'akari da ma shine qashin bayan tattalin arzikinta.
In man ya dan yi farashi mai gwafi-gwafi, kasar zata sami kudin ayyukan ci gaban kasa, da ma na tara wa a lalita wanda zai sanya darajar Naira ta dan yi sama kan sauran kudaden hada-hada na duniya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng