Abin tausayi: Yara biyu sun hadu da ajalinsu yayin da suka tafi wanka a kududufi
Wasu matasa maza guda biyu sun rasa rayyukansa yayin da suka tafi wanka a wata kududufi da ke kauyen Gantsa a karamar hukumar Buji da ke Jihar Jigawa.
Kakakin hukumar tsaro na NSCDC na jihar, Adamu Shehu ne ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) afkuwar lamarin a jiya Juma'a.
KU KARANTA: Hadamarku ta yi kamari - Shugaba Buhari ya fadawa 'yan majalisa
Shehu ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis.
Kakakin ya ce sunayen yaran Yusuf Adamu mai shekaru 6 da Umar Ibrahim mai shekaru 4, bayan likita ya tabbatar da rasuwarsu.
Hakan yasa ya gargardi iyaye da su kara sanya idanu a kan wuraren da yaran su ke zuwa domin kare afkuwar irin haka a gaba.
Idan ba manta ba, a ranar 7 ga watan Disamban 2017, NAN ta ruwaito cewa wasu yan mata hudu sun rasu yayin da suke kokarin tsallaka wata kududufi a kauyen Sakwaya da ke karamar hukumar Dutse.
Kazalika, a ranar 8 ga watan Yulin 2017, Hukumar yan sandan Jihar ta bayar da sanarwan cewa a kalla mutane 11 sun suka rasu sakamakon nutsewa a rafi a cikin wata guda a sassa daban-daban na Jihar Jigawa kamar yadda kakakin hukumar SP Abdu ya sanar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng