Najeriya zata rasa dala $500m ga harkar man fetur a bana, duba dalili

Najeriya zata rasa dala $500m ga harkar man fetur a bana, duba dalili

- Tace NPA tayi asarar dala miliyan 234.4 da Naira biliyan 3.2 sakamakon rage kashi 50 na kudin man fetur daga 2009 zuwa 2015

Manajan ta kara da cewa, a 2018, dala miliyan 561.2 da Naira miliyan 334.2 za a iya asara saboda wannan dalilin

Najeriya zata rasa dala $500m ga harkar man fetur a bana, duba dalili
Najeriya zata rasa dala $500m ga harkar man fetur a bana, duba dalili

Manajar daraktar tashar gabar tekun Najeriya, watau Nigerian Ports Authority (NPA), Hadiza Usman, tace Najeriya zata yi asarar kusan dala miliyan 561.2 da kuma Naira miliyan 34.2 in dai aka yarjewa ragun kashi 50 cikin dari na kudin shigo da man fetur.

Usman ta bayyana hakan ne a gurin taron bayanin kasafin kudi na 2017 da kare kasafin kudi na 2018 na hukumar NPA da kwamitin majalisar wakilai a Abuja.

Ta bada shawarar da tace a kara dubawa dai.

Tace NPA tayi asarar dala miliyan 234.4 da Naira biliyan 3.2 sakamakon rage kashi 50 na kudin man fetur daga 2009 zuwa 2015.

Manajan ta kara da cewa, a 2018, dala miliyan 561.2 da Naira miliyan 334.2 za a iya asara saboda wannan dalilin.

DUBA WANNAN: Najeriya 2-0 Iceland

"Idan munyi wannan asarar, saboda mene bazamu kiyaye ba? Amma yan Najeriya su sani, za a samu ragowa a kudin man fetur. Domin an ba NPA umarnin rage kashi 50 cikin dari na duk wani man fetur da zai shigo kasar."

Shugaban kwamitin, Patrick Asadu, ya hori duk wasu cibiyoyin gwamnati da kada suyi kasa a guiwa da aiyukan su saboda zaben 2019 dake gabatowa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng