Rashin Imani: An karɓe Mata yara 3, an ajiye mata Rago, bakin ciki ya kashe ta a Zaria

Rashin Imani: An karɓe Mata yara 3, an ajiye mata Rago, bakin ciki ya kashe ta a Zaria

Wani lamari mai ban tausayi ya faru a garin Zaria na jihar Kaduna, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wata Mata da aka yi awon gaba da yayanta guda uku, aka maye mata gurbinsu da wani Ragon layya, kamar yadda Legit.ng ta samu tabbataccen bayani.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a cikin watan Azumi, inda wani matashi mai mummunan nufi ya yi sallama da wannan mata, inda ya fada mata wai Mijinta yace ta bashi yaransu guda uku, ciki har da na goye, zai kai su wajen aski.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 35, sun kashe 25

A cewar mutumin, mahaifin yaran na can yana jiransa a shagon askin, haka zalika ya ajiye mata wani katon Rago wanda yace mata mahaifin yaran ne ya aiko shi ya kawo mata, Allah bashi idan an gama yi musu askin zai dawo dasu gida da kansa.

Haka kuwa aka yi, ganin an aiko shi da Rago, hakan ya bata tabbacin da gaske ne, Maigidannata ne ya aiko mutumin, nan da nan ta mika masa Yara uku, ta kama Rago ta daure a cikin gida.

Sai dai tafiyar wannan mugun mutum keda wuya sai ga Maigida ya dawo, ganin bata ganshi tare da yaran ba, mamaki ya kamata, tana tambyarsa ina Yara yana tambayarta wasu Yara, ba tare da wata wata ba ta fayyace masa yadda suka yi da wannan mutumi.

Jin hakan ya tayar da hankulansu gaba daya, inda Maigidan ya bayyana mata shi bai aiki kowa wajenta ba, kuma ma ai da da gaske ne da ya kirata ta wayar salula da kansa, nan take matar ta fadi a sume, haka tayi ta suma a duk lokacin da ta kalli ragon nan, har sai da ta rasu bayan kwanaki uku da faruwar lamarin.

Zuwa yanzu dai babu labarin yaran, balle mutumin, fatan shi ne Allah Ya shiga tsakanin nagari da mugu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: