Na shirya sanya kafar wando daya da Gaidam – Sanata Bukar Abba
Wani Sanata da ya hau kujerar mukami sau uku, Bukar Abba Ibrahim yace a shirye yake ya kara da Gwamna Ibrahim Gaidam wajen neman kujerar sanatan Yobe maso gabas a 2019.
Jaridar Daiy Trust ta rahoto cewa gwamnan wanda ya fito daga mazaba daya da Sanata Ibrahim, na da kudirin takarar neman wannan kujera a majalisar wakilai.
Da yake jawabi ga manema labarai Bukar yace zai sake neman wannan kujera a zaben 2019.
“Ni dai na san cewa shi (Gaidam) bai fada mani ba. Sannan kuma ya san cewa ina son na dawo majalisar dattawa. Idan ya so ya kara ne dani, toh na shirya masa,”inji shi.
A lokutan baya da suka shige yace zai janye kudirinsa na neman kujerar sanata idan Gaidam ya nuna ra’ayi akan kujerar.
KU KARANTA KUMA: Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani
Sanatan wanda ya ajiye kudirinsa na takarar shugabancin kasa don marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a 2015 yace zai nemi kujerar shugabanci idan wa’adin mulkin Buhari ya cika.
Yace majalisar dattawa ban a matasa bane amma yana da kyau a samu cudanya na matasa da tsoffi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng