Ni ma zan fito takarar shugaban kasa a APC – wani Sanata daga arewacin Najeriya

Ni ma zan fito takarar shugaban kasa a APC – wani Sanata daga arewacin Najeriya

Bukar Abba Ibrahim, sanatan Najeriya mai wakiltar jihar Yobe ta gabas, ya bayyana cewar yana da sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasa amma fa sai a shekarar 2023 bayan shugaba Buhari ya kamala zangon san a biyu.

Ni ma zan fito takarar shugaban kasa a APC – wani Sanata daga arewacin Najeriya
Sanata Bukar Abba Ibrahim

Bukar na wadannan maganganu ne yau, Alhamis, a wurin kaddamar da wani littafi da ya rubuta mai taken “Poorlitics: The story of the Little boy from Goniri, and The Progressive Manifesto”.

DUBA WANNAN: “Zan so na sace shi zuwa APC “ –Shugaba Buhari ya na son ganin wani sanatan PDP ya koma APC

Bukar ya bayyana cewar kada ‘yan Najeriya su ga laifin Buhari idan ba a samu dammar kaddamar da dukkan aiyukan dake cikin kasafin kudin bana ba tare da sanar da jama’a cewa,dama ko a baya ba a iya cimma dukkan aiyukan dake cikin kunshin kasafin kudin kasa.

Kazalika, Bukar, ya kare cushen da ake zargin ‘yan majalisar da yi a cikin kasafin kudin bana tare da bayyana cewar, ba wani abu bane don sun kara wasu aiyuka da zasu amfani jama’a cikin kasafin kudin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel