Kuma dai: an kwashi gawarwakin mutane 4 bayan da yan bindiga suka kai hari jihar Filato

Kuma dai: an kwashi gawarwakin mutane 4 bayan da yan bindiga suka kai hari jihar Filato

Akalla mutane hudu ne suka gamu da ajalinsu a hannu wasu gungun yan bindiga dadi da suka kai wani mummunan hari a garin Gashes dake cikin karamar hukumar Barikin Ladi, na jihar Filato, inji rahoton jaridar Premium Times.

Wasu mazaunan garin,Chuwang Moses, da Yohana Samson sun tabbatar da faruwar harin ga majiyar Legit.ng inda yace jama’an garin tarwatsewa suka yi zuwa cikin daji a lokacin da maharan suka dira garin.

KU KARANTA: Mai dokar bacci ya buge da gyangyandi: Labari wasu jami’an tsrao guda 5

Haka zalika shima Kaakakin rundunar Yansandan jihar Filato, Terna Tyopev ya tabbatar da harin, inda yace yan bindigan sun kai harin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni, sai da yace bas hi da tabbacin adadin mutanen da suka mutu.

Daga karshe Kaakaki Terna yace sun aika da wani jami’in Dansanda mai mukamin DPO don bin diddigin lamarin, kuma zai kai rahoto zuwa shelkwatar Yansandan jihar

A wani labarin kuma, Yanbindiga sun kai hari garin Kwal dake cikin karamar hukumar Bassa na jihar Filato, inda suka kashe mutane hudu yan gida daya, a daren Talata, 19 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel