Mai dokar bacci ya buge da gyangyandi: Labari wasu jami’an tsrao guda 5

Mai dokar bacci ya buge da gyangyandi: Labari wasu jami’an tsrao guda 5

Wasu matasa guda biyar dake aiki da wani kamfanin wutar lantarki a matsayin jami’an tsaro sun buge da nuna halin bera, inda aka kama su dumu dumu da satar wayoyin wutar lantarki da darajarsu ta kai naira miliyan biyu da dubu dari biyu da arba’in.

Jaridar The Nation a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni ne jami’in Dansanda mai shigar da kara, Sajan Michael Unah ya tasa keyar mutanen su biyar gaba watan Kotun majistri dake Ikeja na jihar Legas.

KU KARANTA: Tausayi: Buhari ya zubar da hawaye yayin ganin tsabar barnar da gobara ta yi a kasuwar Azare

A yayin zaman Kotun, Dansandan ya bayyana sunayen wadanda ake tuhuma kamar haka; Oluwaseye Oladokun, Chukwuka Peters, Austin Omoh, Tony Oruamen, da Timothy Chuckwudi, inda yake tuhumarsu da laifka biyu kacal, hadin kai cikin laifi da kuma sata.

Dansandan yace mutanen biyar sun hada kai ne da wasu jami’an kamfanin su biyar dake aiki a sashin ajiyan kayayyaki, inda suka saci wayoyi a tsakanin watan Feburairu da watan Mayu, sai dai a yanzu haka jami’an sun ranta ana kare.

Laifukan da ake tuhumar mutanen da aikatawa ya saba da sashi na 287 da 411 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Legas, wanda ya tanadar da hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 9 a jimlace.

Sai dai wadanda ake tuhuma sun musanta tuhume tuhumen, daga nan ne Alkalin Kotun, A.A Fashola ya bada belinsu akan kudi naira dubu dari biyu da hamsin kowanne, sa’annan y adage karar zuwa ranar 11 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: