Yanzu – yanzu: Sama ko kasa, an nemi alkalin da zai shari’ar El-Zakzaky an rasa

Yanzu – yanzu: Sama ko kasa, an nemi alkalin da zai shari’ar El-Zakzaky an rasa

- Har yanzu ana jika kan batun shugaban mabiya Shi'a El-Zakzaky

- Domin alkalin da zai zauna zaman shai'ar bai bayyana ba

Rashin bayyanar mai shari’a Gideon Kurada domin sauraren shari’ar shugaban mabiya mazabar Shi’a El-Zakzaky da matarsa da ya gamu da cikas a dalilin rashin bayyanar alkalin

Yanzu – yanzu: Sama ko kasa, an nemi alkalin da zai shari’ar El-Zakzaky an rasa
Yanzu – yanzu: Sama ko kasa, an nemi alkalin da zai shari’ar El-Zakzaky an rasa

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari tayi shirin aiwatar da titin jirgin kasa da zai zagaye jahohi 9 da Abuja – Amaechi

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta zayyana laifuka takwas da take tuhumar Ibrahim El-Zakzaky da matar shugaban mabiya Shi’an na Najeriya.

Daga cikin laifukan da ake zarginsu da shi sun hada da hada baki wajen kulla kitsattsiya da kin yin katabus gami da tabuka komai wajen kare faruwar rasa rayukan mutane da sauransu.

Amma sai dai an hana ‘yan jarida shiga cikin harabar kotun domin shaida yadda zaman kotun zai kasance.

Lauyan wanda ake kara (Zakzaky) Femi Falana (SAN), ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa, alkalin yana sane ya ki halartar kotun domin sauraren shari’ar

A saboda haka ne lauyan wanda ake kara da kuma lauyan mai karewa sun cimma matsayar dage zaman zuwa 11 ga watan Yuli domin cigaba da shari’ar.

Falana ya kuma nuna ganin baiken jami’an ‘yan sanda na dakatar da ‘yan jarida daga shiga kotun domin ganin yadda zaman zai kaya, domin kuwa a cewarsa babu wata doka da ta hana mutane shaida zaman kowacce shari’a.

An dai gurfanar da Ibrahim Zakzaky da matarsa ne a kotu ranar 15 ga watan Mayu domin fuskantar tumar da ake musu.

Sai dai a wancan lokacin lauyan masu kara Dari Bayero ya bukaci karin lokaci domin samun damar gurfanar da wadanda ake karar tare gaban kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng