Kada Gwamnatin Tarayya ta gina Yankunan Kiwon Shanu da Kudin Al'umma
Wata Kungiyar shugabannin Kudanci da Tsakiyar Najeriya sun bayyana hamayyar su dangane da shirin gwamnatin tarayya na amfani da kudaden al'umma wajen gina yankunan kiwon shanu a jihohi 10 kamar yadda ta bayar da sanarwa.
Kungiyar ta jaddada cewa, kiwon shanu sana'a ce ta ma su zaman kansu, saboda haka gwamnati bai dace ta barnatar da Naira Biliyan 178 na kudaden al'umma wajen samar da yankunan kiwo ga makiyaya wanda su ke sana'o'in su ba tare da biyan wani haraji ba.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Larabar da ta gabata yayin mayar da martani dangane da sanarwar majalisar tattalin arzikin kasa da ta bayyana cewa, gwamnati ta amince da batar da kimanin N179bn domin samar da yankunan kiwon shanu a kasar nan.
KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku shine zabin da zai sanya Najeriya ta fuskanci Alƙiblar ta - Ben Bruce
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ware kasafin Naira Biliyan 70 domin samar da yankunan kiwon shanu a jihohin Oyo, Benuwe, Nasarawa da kuma wasu jihohi bakwai zuwa karshen watan Yulin 2019.
A yayin haka kuma a ranar Talatar da ta gabata ne wata Kungiyar Musulmi a jihar Benuwe, ta kirayi gwamnatin tarayya akan ta kara kaimi wajen goyon bayan samar da yankunan kiwo a kasar nan.
Shugaban wannan kungiya ya yi wannan kira ne yayin da suka kai ziyara ta gaisuwar Sallah ga gwamnan jihar, Samuel Ortom.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng