'Yan majalisar Tarayya sun kasa kare N140b da zasu ci kan aikin dumama kujera

'Yan majalisar Tarayya sun kasa kare N140b da zasu ci kan aikin dumama kujera

- Sun ware wa kansu kaso mai tsoka don aikin zama a kujeru

- Majalisun kasar nan kan kutse cikin kasafin kudi su saka kudaden ayukan da suke so ayi musu

- Sun kasa kare aikin da zasu yi da kudaden

'Yan majalisar Tarayya sun kasa kare N140b da zasu ci kan aikin dumama kujera
'Yan majalisar Tarayya sun kasa kare N140b da zasu ci kan aikin dumama kujera

Majalisar wakilai ta kare majalisar dattawa akan kasafin kudin 2018 daga Naira biliyan 125 zuwa Naira biliyan 139.5.

A bayanin su, dattawan sun ce kasafin yayi kadan Idan aka danganta shi da na shekara 10 da suka wuce. Sun kasa bayyana dalilin da yasa aka kara biliyoyin nairori akan kasafin.

Wannan ya biyo bayan magana da shugabannin majalisar sukayi akan nuna damuwar da shugaban kasan yayi akan karin kasafin kudin.

An san yan majalisar da yin bawa kansu wasu alawus marasa dalili, wanda a cikin kasafin babu wani alawus nasu. Wannan yana nufin sun saka alawus din ne a cikin sauran kasafe kasafen wanda zasu cire su daga baya.

DUBA WANNAN: Hutun sallah ya sauko da kasuwannin hannayen jari daga tiriliyan tara da doriya

Shugaban kasan yace, ya fitar da kasafin kudin tun a watan nuwamba na 2017, wanda ya nuna da wuri akayi kasafin.

Majalisar dai tana mika godiyar ta ga shugaban kasar na sa hannu da yayi akan kasafin. Domin kuwa aiyukan da za a gabatar zasu taba rayuwar mutane saboda dama mutane suke wakilta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel