Kunnenka nawa? Za’a halasta noma da shan tabar wiwi a kasar Canada
Gwamnatin kasar Canada ta halasta noman tabar wiwi, da shan tabar wiwi a kasar tun daga ranar 17 ga watan Oktoban shekarar 2018, kamar yadda shugaban kasar, Justin Trudeau ya tabbatar a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni.
Legit.ng ta ruwaito hatta majalisun dokokin kasar guda biyu sun amince da dokar noma, sha da ta’ammali da tabar wiwi, inda tuni suka gabatar da dokar da zata tabbatar da halascinsa a kasar.
KU KARANTA: Kafa da kafa: Buhari zai kai ziyarar jaje Bauchi bisa ibtila’in da ta fada ma al’ummar jihar
Da wannan, kasar Canada ta zama kasa ta farko a cikin manyan kasashen Duniya guda bakwai masu karfin tattalin arzikin kasa, G7, da ta fara halasta wiwi, kuma ta biyu a Duniya kakaf, a bayan kasar Uruguay.!
A karkashin wannan sabuwar doka, Dokar ta baiwa duk mutumin da shekarunsua ya kai 18 da ya siya wiwi, ya noma wiwi, kuma ya busa wiwi babu laifi akansa, amma fa ba dayawa ba, dokar ta nuna za’a iya shuka wiwi guda hudu a kowanne gida, kuma mutum zai iya daukar giram da basu wuce Talatin ba.
Ministan kiwon lafiya na kasar Canada, Ginette Petipas ya bayyana jin dadinsa da wanna doka, inda yace a yanzu babu sauran haramcin wiwi a kasar, ya kara da cewa hakan zai baiwa yan kasar yin amfani da wiwi ta yadda ya dace.
Shima shugaba Trudeau ya bayyana cewa ya taba shin sau biyar zuwa shida tare da abokansa, don haka ya jaddada goyon bayansa ga halasta ganyen a kasarsa, inda yace a yanzu babu sauran matsalar yan safarar wiwi, kuma hakan wani mataki ne na kare matasan kasar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng