Uwargidar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, Hajiya Zainab ta rasu

Uwargidar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, Hajiya Zainab ta rasu

Allah ya yiwa Uwargidar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, Hajiya Zainab Nyako rasuwa.

Hajiya Zainab ta rasu babban asibitin tarayya dake Yola bayan yar gajeruwar rashin lafiya a safiyar ranar Laraba tana da shekaru 63 a duniya.

Jaridar Leadership tattaro cewa an kai Zainab Nyako asibitin FMC Yola cikin gaggawa bayan ta yanke jiki ta fadi a ranar Talata da misalign karfe 4:00 na rana sannan ta mutu a asibitin bayan yan wasu dakiku.

Uwargidar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, Hajiya Zainab ta rasu
Uwargidar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, Hajiya Zainab ta rasu

Zainab ta rasu ta bar mijinta Murtala Nyako, yara shida mahaifiyarta da kuma jikoki 10.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah yayiwa tsohon Sufeto Janar na yan sanda Gambo Jimeta rasuwa

Za’ayi jana’izarta a garin Yola bisa ga koyarwar addinin Musulunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng