Na ga shekaranjiya, na kuma ga jiya, Buhari a yau ba zai tayar mun da hankali ba - Obasanjo

Na ga shekaranjiya, na kuma ga jiya, Buhari a yau ba zai tayar mun da hankali ba - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo yace Allah da ya kauda Abacha zai kauda Buhari

- Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya su je su yanki katin jefa kuri'a

- Hakama kuma yace shi da ya ga shekaranjiya da jiya ai Buhari ba zai bashi tsoro ba

Tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya ce shi da ya ga shekaranjiya da jiya ai Buhari ba zai bashi tsoro ba.

Na ga shekaranjiya, na kuma ga jiya, Buhari a yau ba zai tayar mun da hankali ba - Obasanjo
Na ga shekaranjiya, na kuma ga jiya, Buhari a yau ba zai tayar mun da hankali ba - Obasanjo

KU KARANTA: Da kudin barayi Buhari ya ci zaben 2019 - PDP

Haka zalika ya bayyana cewa yanzu haka ya dukufa wajen rokon Allah da ya kaudawa 'yan Najeriya Buhari kamar yadda ya kauda Abacha daga mulki kafin zaben 2019.

Sai dai kuma tsohon shugaban kasar ya shawarci dukkan masu irin ra'ayin sa na korar Buhari daga mulki da su hanzarta su je su nemi katin su na zabe domin aikin da ke gaban su babba ne.

Legit.ng cewa tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da abokan tafiyar sa na gangamin korar Buhari din watau Coalition for Nigeria Movement (CNM) a garin ibadan na jihar Oyo.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng