Katobara: Allah-n da ya yi mana maganin mulkin Abacha, shine zai kara taimakon mu a 2019 – Obasanjo

Katobara: Allah-n da ya yi mana maganin mulkin Abacha, shine zai kara taimakon mu a 2019 – Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo y ace Allah-n day a kawo karshen mulkin shine zai kara yin taimako a zaben 2019 mai zuwa

- Kazalika, ya bukaci ‘yan sabuwar jam’iyyar sat a CNM das u tabbatar sun tanadi katin su na zabe domin samun bayar da tasu gudunmawar kafin barin komai a hannun Allah

- Tsohon shugaban kasar ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar ta sad a kada su karaya ko su ji tsoro

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja da kuma farar hula, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewar ya mika dukkan lamarin fitar da shugaba Muhammadu Buhari daga gidan gwamnati a hannun Allah. Ya bukaci ‘yan jam’iyyar sa da su mallaki katin zabe kafin zaben shekarar 2019.

Obasanjo na wadannan kalamai ne yayin wani taro da ya yi a garin Ibadan na jihar Oyo da ‘yan sabuwar jam’iyyar sa ta CNM (Coalitiona Of Nigeria Movement).

Katobara: Allah-n da ya yi mana maganin mulkin Abacha, shine zai kara taimakon mu a 2019 – Obasanjo
Buhari da Obasanjo

Da yake bayar da misali ga masu sauraron sa, Obasanjo, ya ce haka Allah ya yi maganin Abacha lokacin da ya kafe sai ya cigaba da mulkin Najeriya ta kowanne hali.

wadanda suke a kan karagar mulki basa son a fada masu cewar suna yin ba daidai ba, burin su kawai su cigaba da zama a mulki. Amma idan muka fada masu gaskiya, sai su yunkuro suna masu ganin laifin mu,” a cewar Obasanjo.

DUBA WANNAN: Ka janye sojoji daga Maiduguri, ka tura ‘yan sandan SARS –Kungiyar kishin Najeriya ga Buhari

Sannan ya kara da cewar, “Allah-n da ya taimake mu jiya ya kawar mana da Abacha shine zai taimake mu a zaben gobe na 2019. Amma fa mu ma sai mun bayar da tamu gudunmawar kafin mu bar wa Allah ragowar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng