Gwaggon biri mafi tsufa a duniya ya mutu yana da shekaru 62
Gwaggon biri mafi tsufa a duniya ya mutu yana da shekaru 62 da haihuwa a gidan ajje namun daji na Perth da ke Kasar Ostireliya.
Tun shekarar 1968 gwaggon birin ya ke gidan ajje namun dajin na Perth kuma akwanakin baya tsananin tsufa ya sanya an yi masa allurar barci.
Gwaggon birin mai suna Puan yana da yara 11 da jikoki 54 kuma ana kiran sa da suna tsohon dattijo a gidan gonar.
A shekarar 2016 ne aka bayyana birin a matsayin wanda ya fi tsufa a duniya inda ya shiga littafin tarihi na "Guinness Book of Record."
KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Tsoffin gwamnonin Najeriya shida da aka yankewa hukunci bayan kama su da laifin aikata rashawa
Hukumar Kare Namun Daji ta Duniya ta ce, akwai gwaggon birin nau'in Sumatra dubu 14,600 a duniya baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng