Fasto ya bayar da Gudunmuwar N1m domin Kammala Ginin Masallaci a birnin Calabar

Fasto ya bayar da Gudunmuwar N1m domin Kammala Ginin Masallaci a birnin Calabar

Wani Babban Fasto na Cocin Peniel, Essien Ayi, ya bayar da gudunuwar Naira Miliyan guda ga wata Al'ummar Musulmi domin kammala ginin wani babban masallaci dake cibiyar Musulunci ta babban birnin Calabar a jihar Cross River.

Ayi wanda dan Majalisa ne mai wakilcin wasu mazabu na Kudancin Calabar a Majalisar wakilai ya bayyana cewa, ya kamata 'yan Najeriya su rika taimakon junansu ba tare da la'akari da bambancin addinan su ba.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana Babban Limamin kuma dan Majalisa ya bayar da wannan gudunmuwa ne a wata Mazaunar kabilar Hausawa dake birnin Calabar, inda ya ce ya yi wannan hobbasa ne domin yabawa goyon bayar da suke yi a kansa.

Fasto ya bayar da Gudunmuwar N1m domin Kammala Ginin Masallaci a birnin Calabar
Fasto ya bayar da Gudunmuwar N1m domin Kammala Ginin Masallaci a birnin Calabar

A kalamansa "kowane mutum walau Kirista ko Musulmi ya yarda cewar akwai Allah. Addini na iya zama daban hakazalika hanyar gudanar da bauta kan kasance daban sai dai kowace hanya ta karkata ne zuwa ga bauta ga Ubangiji."

Legit.ng ta fahimci cewa, dan Majalisar ya yi wannan tagomashi ne ga al'ummar sakamakon goyon bayan sa tun yayin da yake rike da kujera ta shugaban karamar hukuma.

KARANTA KUMA: Majalisar Dinkin Duniya ta la'anci hare-haren ƙunar bakin wake na Damboa

Rahotanni sun bayyana cewa, Ayi ya kuma kai ziyara wasu gidaje biyu na Marayu da kuma na tsaffi da suka gajiya inda ya malalar da dukiyar sa wajen bayar da gudunmuwa da agaji.

Ya kara da cewa, a duk sa'ilin da Ubangiji ya wadata ka da arziki kai ma sai ka dubi na kasa da idanun jin kai wajen taimako da bayar da tallafi.

Shugaban al'ummar Hausawa na yankin, Sarki Lawan, ya bayyana cewa wannan gudunmuwa da dan majalisa Ayi ya bayar za ta taimaka matuka wajen kammala ginin masallacin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel