Fasaha: Wani Almajiri yana kera keken sayarwa a jihar Borno

Fasaha: Wani Almajiri yana kera keken sayarwa a jihar Borno

Yayinda matasa masu digiri da digir-gir ke kuka kulli yaumin kan rashin aikinyi da kuma zaman kashe wando, wani matashi wanda akace yayi almajiranci a da ya samawa kansa aikinyi ba tare da sauraron gudunmuwar gwamnatin tarayya.

Wannan matashi mai suna Umar wanda ke wannan abun arzikin a hanyar tafkin Chadi da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno yana kera kekunan yara domin sayarwa tamkar wandanda ake shigo da su daga kasahen ketare.

Fasaha: Wani Almajiri yana kera keken sayarwa a jihar Borno
Fasaha: Wani Almajiri yana kera keken sayarwa a jihar Borno

Irin wannan abu da wannan matashi ke yi nuni ne ga cewa ba wajibi bane mutum ya yi karatun jami’a kafin yayi amfani da fasahar da Allah ya bashi.

KU KARANTA: Saboda tsoron mahafiya, yarinya ta hallaka kanta

Kana wannan abu kira ne ga iyaye da malamai su taimakawa yara wajen koya musu aikin hannu duk da zuwa makaranta domin taimakawa kansu bayan kamala karatu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel