Sojin Sama run fara ruwan wuta kan sansanonin 'yan fashin Zamfara
- Kashe-kashen Zamfara sunyi qamari
- Sabbin jami'an tsaro sunyi dirar mikiya a jihar
- An fara luguden wuta kan makasan jama'a
Sojojin sama na najeriya sun fara ruwan bama baman sama a ranar litinin, a hadin guiwar sojojin don kawo karshen ta'addanci a Zamfara.
Kwamandan kungiyar maida martanin gaggawa ta sojojin sama, kaftin Caleb Player, ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau.
Yayi maganar ne bayan an kai jiragen sama biyu domin aikin.
Olayera ya bayyana aikin a matsayin wani bangare na aikin hadin guiwa da ya kunshi sojojin sama, na kasa da kuma yan sanda don kawo karshen ta'addancin.
Ofishin dillancin labarai na NAN, ya ruwaito cewa jihar zamfara a cikin jihohin arewa maso yamma tana fama da yan ta'adda a kwanakin nan inda ta'addancin ke kawo rashin daruruwan mutane, yana kuma korar mutane da yawa daga gidajen su.
Gwamnatin tarayya tana ta yaki da Boko Haram a arewa maso gabas wanda yayi sanadiyyar lashe dubban rayuka da kuma korar miliyoyi tun shekarar 2009.
Olayera ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba zaman lafiya zai dawo jihar domin sun shirya tsaf don yakar yan ta'addan.
DUBA WANNAN: Abubuwa 12 da matatar mai ta Dangote ta kafa
Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya bayyana damuwar shi akan ta'addancin, ya bayyana matsayin shi na shugaban tsaro na jihar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng