Abin ya zo: Laftanar janar Buratai ya kaddamar da fadan karshe akan Boko Haram (Hotuna)

Abin ya zo: Laftanar janar Buratai ya kaddamar da fadan karshe akan Boko Haram (Hotuna)

Babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya kaddamar da aiki na musamman don shirya fadan karshe da kungiyar ta’addanci na Boko Haram, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kaakakin rundunar Sojin kasa, Birgediya Texas Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuni, a garin Monguno na jihar Borno, inda ya bayyana manufar aikin ‘Operation Last hold’ shi ne kakkabe ragowar yan Boko Haram daga yankin don baiwa yan gudun hijira damar komawa gidajensu.

KU KARANTA: Takarar Gwamna:Kwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wuya ba – Inji Kabiru Marafa

Buratai wanda ya samu wakilcin shugaban horaswa na rundunar Sojin kasa, Manjo Janar David Ahmadu, ya bayyana karasa har garin Gudunbali, tare babban kwamandan yaki da Boko Haram, Nicholas Rogers inda suka gudanar da sharar gona dake alanta manufarsu na kakkabe ragowar yan ta’adda.

Da yake jawabi, Buratai yace sharar da suka yi na bayyana bukatarsu na ganin sun samar da dawwaamammen zaman lafiya a yankin da zai baiwa yan gudun hijira komawa garuruwansu, inda manoma zasu samu damar cigaba da gudanar da nomansu.

Haka zalika, a ganawar da yayi da wasu yan gudun hijira da suka koma garinsu bayan kwashe shekaru da dama a karamar hukumar Guzamala, Buratai yace wannan shine mataki na farko na ganin dukkanin yan gudun hijira sun koma gida.

Daga karshe yayi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu dasu basu cikakken gudunmuwa don ganin sun cimma wannan kyakkyawar manufa da suka sanya a gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel