2019: Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

2019: Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Makarfi, ya bayyana kudirin sa na tsayawa takarar shugabancin kasa.

Makarfi dai zai nemi wannan kujera ne a karkashin lemar babban jam’iyyar adawar kasar wato PDP.

Ya bayyana wannan kudiri na sa ne a wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a gidan sa dake Kaduna, a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuni.

Ya jaddada cewa kafin ya yanke tunanin tsayawa ko ayyana fitowa takarar, sai da ya tuntubi jama’a da dama a fadin kasar nan.

2019: Makarfi ya fito takarar shugaban kasa
2019: Makarfi ya fito takarar shugaban kasa

Sai dai kuma inji shi, wannan ba wai ya na nufin shi ne dan takarar da jam’iyyar gaba daya ta amince da shi ba.

KU KARANTA KUMA: Sanata yayi rabon N500 a matsayin rarar Dimokradiyya (hotuna)

Ya kara da cewa ya kara fahimtar halin da Najeriya ke ciki, ta hanyar yawon tuntubar jama’a da ya yi domin neman shawarar su ta batun tsayawar sa ta kara.

A halin da ake ciki, Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya ya kaddamar da kudirinsa na takara inda zai kara da gwamnan jihar Kaduna mai ci, Mallam Nasir El-Rufai, a zabe mai zuwa na 2019.

Haka zalika anyi zargin cewa Sani ya ba da haske akan kudirinsa na barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

acebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng