Kaico! Yan bindiga a jihar Zamfara sun guntule ma wani mutumi hannu (Hotuna)
Ayyukan yan bindiga na cigaba da kamari a yankunan garuruwan jihar Kaduna, Zamfara da Katsina, musamman ma a jihar Zamfara inda a yanzu haka yan bindigan sun yi sanadiyyar mayar da mutane da dama a jihar yan gudun hijira.
Jaridar Rariya ta ruwaito a wani hari da yan bindigar suka kai a cikin yan kwanakin nan, yan bindigan sun guntule hannun wani matashi, hannunsa na hagu, a kauyen Bula dake cikin karamar hukumar Shinkafi na jihar.
KU KARANTA: Yadda Gawar wata Mata ta hallaka Dan cikinta a yayin da ake tsaka da jana’iza
hakazalika Legit.ng ta ruwaito a sakamakon hare haren yan bindigar, mazauna kauyukan dake gefen garin Gusau sun fice daga kauyukansu don tseratar da rayuwarsu, inda suka shigewa garin Gusau, wasu kuma zuwa jihar Katsina.
Wani rahoto ya bayyana cewa wadanda basu samu wajen zuwa ba, suna kwanciya ne a cikin kogunan duwatsu don tseratar da ransu, yayin da wasu kume ke darewa kan bishiyu.
Sai dai wani abun bacin rai shi ne duk wannan mawuyacin hali da al’ummar jihar Zamfara ke ciki, sai ga shi gwamnan jihar Abdul Aziz Yaro yari ya dauki nauyin wasu manyan jami’an gwamnatinsa guda biyar zuwa kasar Rasha don kallon gasar cin kofin Duniya na kwallon kafa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng