Wata jami'ar Najeriya ta dakatar da wani dalibi bayan yayi tone-tone a hira da 'yan jaridu

Wata jami'ar Najeriya ta dakatar da wani dalibi bayan yayi tone-tone a hira da 'yan jaridu

- Ana yawan samun labarun malaman jami'a na kokarin fyade ga mata don maki

- Wata budurwa tayi tone-tone sai dai jami'ar bata ji dadi ba

- An dakatar da ita zuwa ayi bincike kan rahoton

Wata jami'ar Najeriya ta dakatar da wata daliba bayan tayi tone-tone a hira da 'yan jarudu
Wata jami'ar Najeriya ta dakatar da wata daliba bayan tayi tone-tone a hira da 'yan jarudu

Jami'ar Ibadan dake jihar Oyo, ta dakatar da dalibi shekara daya, hukunci da ta zartas kan wai ya yiwa jami'ar qage da tonon silili, da ma rubutu ga 'yan jarida shekaru biyu da suka shude. Hkumar jami'ar ta yanke hukuncin a makon jiya.

Tone tonen da yayi, sun hada da rashin tsarin makarantar, da wai rashin ababen more rayuwa, musamman a dakuna, da cin hanci da rashawa.

Wasu karin tone-tonen, sun hada da wai yadda ake rabon maki ga dalibai da ake soyayya dasu, da ma kuma yadda karatun ya tabarbare don malaman basu iya aiki ba.

DUBA WANNAN: Budaddiyar Wasika zuwa ga HAmza Al-Mustapha

Dalibin, Adekunle Adebajo, wanda yanzu yana aji biyar a makarantar koyon lauya ta jami'ar tarayya dake Ibadan.

A watannin da suka gabata dai, an sami irin wannan inda tone-tone suka nuna wani Farfesa yana neman a bashi damar saduwa kafin ya bari a ci kwas dinsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng