Hotunan wata mata da aka gano a cikin wani katon maciji bayan kwanaki da bacewar ta
Wani abun al'ajabi da ya faru a kasar Indonesia da ya ke daukar hankalin duniya yanzu haka shine na wata mata da aka gani a cikin cikin wata kaduwar macijiya da aka yanka bayan kwanaki da bacewar ta.
Kamar dai yadda majiyar mu ta bayyana, an gano matar ne a yayin wani binciken kwakwaf da akeyi domin nemo matar a yankin Sulawesi dake a kudu maso yammacin kasar.
KU KARANTA: Ku kara hakuri, gyaran Najeriya sa a hankali - Buhari
Legit.ng ta samu cewa matar dai sunan ta Wa Tiba kuma shekarun ta 54 a duniya. Mun samu haka zalika cewa 'yan garin dai sun fara zargin macijiyar ne da hadiye matar bayan da suka ga wasu kayayyakin ta a kusa da ita.
To cikin ikon Allah kuwa suna kashe macijiyar suka buda cikin ta sai ga matar a mace a ciki amma babu alamar lahani a jikin nata.
A watan Maris ma dai na shekarar bara, kafafen yada labarai sun ruwaito cewar wata macijiyar ta hadiye wani mutum a gonar sa a kasar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng