Masuburbudar wuta a Najeriya sunyi mutuwar kasko a karon farko cikin watanni 4

Masuburbudar wuta a Najeriya sunyi mutuwar kasko a karon farko cikin watanni 4

Yanzu haka dai labarin da muke samu na nuni ne da cewa matsalar wutar lantarkin da ake fama da ita a Najeriya ta samo asali ne a sanadiyyar lalacewar tashoshin samar da wutar baki dayan su.

Sai dai kamar yadda muka samu, wannan shine karon farko da hakan ta taba faruwa tun a watan Fabreirun da ya gabata kimanin watanni hudu kenan.

Masuburbudar wuta a Najeriya sunyi mutuwar kasko a karon farko cikin watanni 4
Masuburbudar wuta a Najeriya sunyi mutuwar kasko a karon farko cikin watanni 4

KU KARANTA: An kai wani matashi kotu nisa laifin taba nonon matar aure

Legit.ng dai ta samu cewa tashoshin wutar da suka lalace a halin yanzu dai sun hada da Sapele I, Geregu I, Sapele II da kuma Alaoji.

Daman kuma a can baya tashohin Afam IV da V, Geregu II, Olorunsogo II, Odukpani II, Gbarain, AES, ASCO, Omoku, Trans-Amadi da kuma tashar da ke jihar Ribas duk sun lalace.

Yanzu dai kamar yadda muka samu an fara shawo kan matsalar kuma harkar wutar lantarkin zata habaka nan ba da dadewa ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng