Jiga-jigan 'yan siyasa 13 da Buhari ya daure tun daga hawan mulkin sa a 2015

Jiga-jigan 'yan siyasa 13 da Buhari ya daure tun daga hawan mulkin sa a 2015

Ko shakka babu daya daga cikin alkawurran da shugaba Buhari ya dauka yayin yakin neman zaben sa shine na yaki da cin hanci da rashawa - wadda yace idan dai har Najeriya ba ta yake ta ba ta kuma kashe ta, to ita lallai ne za ta kashe kasar.

To sai dai kawo yanzu wasu na ganin tabbas shugaban kasar ya tabuka abun azo-a-gani musamman a harkar na yakin da rashawa musamman ma irin yawan mutanen da ya gwamnatin ta shugaban kasar ta kama.

Jiga-jigan 'yan siyasa 13 da Buhari ya daure tun daga hawan mulkin sa a 2015
Jiga-jigan 'yan siyasa 13 da Buhari ya daure tun daga hawan mulkin sa a 2015

KU KARANTA: Wata jam'iyya ta sha alwashin canzawa Najeriya suna in ta lashe zaben ta a 2019

Ko da yake da wasu 'yan kasar na ganin cewa har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba, wasu kuma gani suke yi kamar gwamnatin ta shugaba Buhari na anfani ne da sunan yaki da cin hancin wajen yakar 'yan adawa kawai.

Legit.ng ta tattaro maku wasu daga cikin jiga-jigan 'yan siyasar da gwamnatin ta shugaba Buhari ta yi sanadiyyar zuwan su gidan yari tun daga shekarar 2015 da ya hau mulki:

1. Babangida Aliyu

2. Mukhtar Ramalan Yero

3. Jonah Jang

4. Bala James Ngilari

5. Joly Nyame

6. Sanata Nwaoboshi

7. Sule Lamido

8. Oliseh Metuh

9. Bala Muhammad

10. Dino Melaye

11. Sambo Dasuki

12. Femi Fani Kayode

13. Joshua Dariye

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel