Rashin Cika Alkawari ya sanya na kashe Ubangida na Ma'akacin Sojin Ruwa da Budurwar sa

Rashin Cika Alkawari ya sanya na kashe Ubangida na Ma'akacin Sojin Ruwa da Budurwar sa

Wani yaran gida ya kashe Ubangidan sa Ma'akacin Sojin Ruwa, Laftanar Abubukar Yusuf dan shekara 35 tare da Budurwar sa, Lorraine Onye a Kudancin kasar nan ta Najeriya.

Bayan shaƙe wuyan Onye har sai da ta daina numfasawa, wannan yaran gida Raphael Jaja, ya kuma soke Yusuf har lahira yayin da yake bacci inda ya nade gawar sa cikin jaka kuma ya garzaya da ita wani daji ya banka mata wuta.

Wannan yaran gida dan asalin karamar hukumar Opobo ta jihar Ribas, ya yanke wannan hukunci ne na salwantar da rayuwar masoyan biyu yayin da ubangidan sa ya ki biyan sa albashi har na tsawon watanni 15 amma ya iya sayen wayar salula mai tsadar gaske ga Budurwar sa tare da biya ma ta kudin hayar gida har N300, 000.

Rashin Cika Alkawari ya sanya na kashe Ubangida na Ma'akacin Sojin Ruwa da Budurwar sa
Rashin Cika Alkawari ya sanya na kashe Ubangida na Ma'akacin Sojin Ruwa da Budurwar sa

Yake cewa, ubangidan na sa ya ma sa alkawarin taimako na ajiyar albashin sa da yake N15, 000 a kowane wata da zai biya shi lokaci guda domin samun dama ta yin aure.

Wannan lamari ya jefa Jaja cikin damuwa tare da fusata shi yayin da marigayi Yusuf ya saba wannan alkawari da ya dauka.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke Mutane 20 'Yan Kungiyar asiri a jihar Akwa Ibom

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, Ma'aikacin sojin ruwan ne ya kashe Budurwar sa kuma ya arce abinsa yayin da yanzu bincike da sanadin jagoran Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda, Abba Kyari, ya bankado gaskiyar lamarin wannan ta'addanci.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sanda ta bankado gaskiyar wannan lamari ne ta hanyar wayar Salula ta Marigayi Yusuf da Jaja ya sayarwa wani abokin sa a birnin Fatakwal inda aka yi ram da shi a ranar Litinin 4 ga watan Yuni.

Wani jami'in dan sanda ya shaidawa manema labarai cewa, Jaja ya amsa laifin sa baya ga jagorantar su zuwa ga barbashin da ragoye-ragoye na gawar Ma'aikacin Sojin a dajin da ya kone ta tare da ta Motar sa kirar Hyundai Veloster da sayar akan Naira Miliyan 1.9.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng