Yadda na ki yarda da shawarar na ajiye azumin watan Ramadana – Shugaba Buhari

Yadda na ki yarda da shawarar na ajiye azumin watan Ramadana – Shugaba Buhari

A yau, juma’a, shugaba Buhari ya ce ya ki daukan shawarar da aka ba shi na kada ya yi azumin watan Ramadana.

Duk da bai bayyana ko wanene ya bashi wannan shawara ba, shugaba Buhari ya ce bayan kamala azumin watan ramadana, lafiyar sa ta karu fiye da baya.

Buhari na wannan kalamai ne yayin karbar bakuncin mazauna Abuja, karkashin jagorancin ministan Abuja, Mohammed Bello, yayin da suka kai masa gaisuwar barka da sallah a fadar gwamnati.

Yadda na ki yarda da shawarar na ajiye azumin watan Ramadana – Shugaba Buhari
Shugaba Buhari a masallacin Idi

Tawagar mutanen sun hada da ‘yan majalisa, malaman addini, wasu daga cikin hadiman sa, shugabannin hukumomin tsaro da sauran su.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa nake murna da binciken da EFCC ke yi a kai na - Babachir

Ina matukar godiya ga malamai da limaman coci da suka zo don yi min barka da sallah bayan kamala azumin watan Ramadana,” a cewar Buhari.

Sannan ya kara da cewa, “waccan shekarar ban samu dammar yin azumi ba saboda rashin koshin lafiya. Amma wannan shekarar na yi azumi gabadaya kuma naji dadin hakan, ina godiya ga Allah.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel