Mutuwa mai yankan kauna: Hukumar shige da fice ta kasa tayi babban rashi
Hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta bayar da sanarwar mutuwar mataimakin shugabanta na kasa mai kula iyakoki, DCG Raymond Tonye Akra Jaja.
A wani jawabi da kakakin hukumar, Sunday James, ya fitar a jiya, Alhamis, hukumar ta bayyana cewar DCG Jaja ya mutu ne ranar 9 ga watan Yuni da muke ciki bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
Shugaban hukumar NIS na kasa, Muhammad Babanded, ya bayya a marigayin a matsayin mutum maid da’a da hukumar zata dade bata manta da shi ba.
Shugaba Buhari ya yi kira ga musulmi da su dore da halayen kirki har bayan azumin watan Ramadana mai alfarma. Bayan hakan, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su raba addini da tarbiya, domin a cewar sa, yin hakan zai bayar da kafa ga balagurbin shugabanni.
DUBA WANNAN: Karanta goron Sallah daga shugaba Buhari
A cikin sakon nasa, ga musulmi, na kammala azumi, shugaba Buhari ya yiwa musulmi murnar ganin watan Ramadana tare da bukatar su zama masu koyi da kyawawan halayen masu azumi domin zama wakilan Musulunci na kwarai.
Shugaba Buhari Kazalika, shugaba Buhari ya nuna takaicin sa bisa yadda son kai da hadama suka yi katutu a zukatun mu hart a kai ga wasu na mancewa da tarbiyya saboda hakan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng