Babban dalilina na cewa Buhari yayo murabus- Sheikh Gumi

Babban dalilina na cewa Buhari yayo murabus- Sheikh Gumi

Fitaccen malamin islaman nan mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Dakta Ahmad Gumi ya bayyana cewa shi fa har yanzu yana nan kan bakan sa na cewa ya kamata Shugaba Buhari yayi murabus saboda gazawar sa karara a wajen yadda yake tafiyar da mulkin kasar nan.

Fitaccen malamin dai yayi wannan kalamin ne a yayin da yake rufe wa'azin watan Ramadan na wannan shekarar a masallacin Sheikh Sanus Khalil dake a unguwar Rigachikun, jihar Kaduna.

Babban dalilina na cewa Buhari yayo murabus- Sheikh Gumi
Babban dalilina na cewa Buhari yayo murabus- Sheikh Gumi
Asali: UGC

KU KARANTA: Yau take Sallah, Allah ya karbi ibadun mu

Legit.ng ta samu cewa haka zalika Dakta Gumi ya karyata zargin da ake yi masa na cewa yana goyon bayan jam'iyyar PDP ne shi yasa yake sukar shugaban kasar inda yace shi bai da jam'iyya.

A wani labarin kuma, Wani babban malamin addinin Kirista a Najeriya mai suna Bishop Osadolor Ochei mai rajin tabbatar da hana cin hanci da rashawa a Najeriya ya bukaci babbar kotun tarayya a garin Abuja da ta sa hukumar EFCC ta binciki tsohon gwamnan jihar Edo.

Shi dai babban malamin ya roki cewa kotun ta sa a binciki tsohon gwamnan Kwamared Adams Oshiomhole ne saboda yana zargin sa da tafka mummunar ta'asa lokacin da yana gwamnan jihar ta Edo shekara takwas.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng