Budaddiyar Wasika zuwa ga Manjo Hamza Al-Mustapha kan 2019
- Jihar Yobe na bukatar masu masaniya ta kan tsaro kamar dai yadda sauran jihohin arewa maso gabas
- Watakil kaine zaka iya shawo kan Boko Haram su daina kwashe 'yaran mutane a makarantu, ko ta sulhu ko ta wuta
- Lokaci ne yanzu na ka ajje khaki in kana dashi, ka shiga siyasa ka ceci yankin ka
Wannan rubutu ra'ayin marubuci ne, ba lallai na shafin jaridar Legit.ng ba
Manjo Al-Mustapha, tun muna yara muke jin labarinka, kan irin jaruntar ka, sanin aiki, kaifin basira, rashin tsoro, sanin hanyoyin tuggu da iya warware su, sanin lungunan masu kulle-kulle, da ma fahimtar sulhu da kuma bada wuta in akwai bukatar hakan.
Manjo, ka fara zama dattijo, ka kai wani matsayi da kaima ya kamata ka bada taka gudummawar, ba daga karkashin inuwar wata giwar ba, a'a, kaima ka kai giwa yanzu, domin in a khaki ne, ka kai Janar ya zuwa yanzu, tunda a tunani na baka yi ritaya a hukumance ba.
Lokaci yayi, da zaka fada tsundum cikin siyasa, domin ka ceto al'ummar mu daga tashin hankali, zalunci, da jahilci a hannun sauran 'yan'uwanmu masu kokarin kafa daular Islama a Arewa, ta karfi da jihadi.
DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga shugaba Buhari kan Almajirci a Arewa
Duk da ni ba dan Yobe bane, kuma ba addininka nake ba, ina matukar kishin jihohin arewa, da yadda muka zamo karkashin ta'addanci da kiyayyar juna, ga kanmu da makwabtanmu abokan zaman mu.
Ko da a Kano kayi takarar gwamna ina tabbatar maka zamu zabe ka, amma kamar dai jihar Yobe tafi bukatar ka a yanzu, kuma ko bakka da kudi ina tabbatar maka mu samari zamu yi karo-karo mu kuma yi maka kamfe kyauta.
Idan kaci gwamna, na tabbatar ka san ta kan tsiyar Boko Haram, na tabbatar zaka iya shawo kan matsalar tsaron jihar, watakil da ma yankin gaba-daya.
Wannan kawai fata ne na gari, ka yafe baya, kaima ka nemi wadanda watakil ka muzgunawa su yafe maka, ka waigi jiharka ta Yobe, ka tsayar da matsalar tsaro daga Boko Haram su daina dauke yaran mutane da sunan jihadi.
Da fatan wasika ta zata isa gare ka, ina kuma yi maka fatan alheri, da Barka da Sallah.
Mubarak Bala,
Dalibin kimiyya a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.
(sms text: +2348032880989).
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng