Wutar lantarki: Dangote zai fara samar da wutar NEPA ga 'yan Najeriya

Wutar lantarki: Dangote zai fara samar da wutar NEPA ga 'yan Najeriya

- Dangote na samar da matatar mai da tai kowacce girma a duniya

- Zai fara samar da lantarki don morar Najeriya

- A yanzu da lantarki da ruwa da mai duk sun gagari mutanen kasar nan

Wutar lantarki: Dangote zai fara samar da wutar NEPA ga 'yan Najeriya
Wutar lantarki: Dangote zai fara samar da wutar NEPA ga 'yan Najeriya

Bututun mai na kungiyar Dangote ana sa ran zai samar da iskar gas da kuma karin Mega Watts 12,000 na hasken wutar lantarki da kuma Mega Watts 570 ga ginin matata.

Ana sa ran bututun ya samar da hanyar fitar da man fetur daga tudu. Da yawan gas din da ake samu a tudu a Najeriya yana bin iska ne.

Dangote yana so ya zamo mai samar da wannan gas din ko siya domin siyarwa.

A bayanin da yayi a taron wannan shekarar na Ghanian international Petroleum (2018),wanda akayi a Accra, babban birnin Ghana.

DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga Hamza Al-Mustapha

Mai bada shawara ga shugaban kasa ta fannin fasaha na kungiyar matatar man fetur ta Dangote, ya jagorance kungiyar matatar zuwa taron, Engr Babajide Soyode, yace;

Aliko Dangote a koda yaushe zai yi iya kokarin shi a kowane bangare na tattalin arziki da yasa gaba, shiyasa za a gama ginin matatar, ta kuma fara aiki don cimma manufofin Najeriya, Afirka ta yamma da duk Nahiyar Afirka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel