Bankin ci-gaban manoma na Afirka zai raba jari na biliyan 500 don habaka noman rogo
- Dr Fregene yace rogo babban abu ne a abincin Africa da kuma samar da arziki ga matasa da mata
- Ya kara da cewa sabon amfanin rogo yazo ne inda ya zama abinci ga yara ko kuma kaji da sauran dabbobi
African Development Bank ya bayyana nufin shi na zuba hannun jarin dala miliyan 120 a shekaru uku masu zuwa don bunkasa samarwa da sarrafa rogo da wasu kayan gona guda 8.
Kayan gonan guda 8 sun hada da :Rogo, shinkafa, masara, dawa, alkama, tumaki, kiwon dabbobin ruwa, jan wake da kuma jan dankali.
Daraktan noma da kiwo na AfDB, Dr Martin Fregene ya bayyana hakan a taron kasashe kashi na hudu a kan rogo, wanda kungiyar hadin guiwa ta habaka rogo na karni na 21, akayi Cotonou, jamhuriyar Benin.
Yace sarrafa rogo a Nahiyar Afirka zai taimaka ma kasashen ta hanyar yanke shigo dashi da kuma samar da dala biliyan 1.2 zuwa asusun tattalin arziki na Afirka.
DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga Hamza Al-Mustapha
A wata hirar ta yan jaridu da aka nuna a IITA, kwararren sadarwa, Godwin Atser yace taron rogon ya samu halartar sama da 450 na masu hadaka a bangaren rogo, wanda ya hada da bincike da cigaban kungiyoyi, Gwamnati, manoma da kuma bangarori masu zaman kansu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng