Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta fara sabuwar sana'a
A dai dai lokacin da ake ta gudanar da shire-shiren bukukuwan karamar sallah a kasashen da dama na musulmai, batun da kan jefa mutane -maza da mata, yara da manya- dayawa cikin zullumi shine na ganin sun mallaki sabon dinkin sallah.
Sai dai ba kowa ne ke samun hakan ba saboda rashin alkawari irin ta teloli da kan saka jama'a da dama cikin kunya sakamakon kin yi masu dinkin Sallar su cikin lokaci.
KU KARANTA: Gobe sallah: An ga wata a Saudiyya
Legit.ng ta samu cewa watakila wannan na daya daga cikin abubuwan da suka tunzura jarumar fina-finan Hausa ta masana'antar Kannywood, Nafisa Abdullahi ta yanke shawarar bude sabon shagon dinki.
Jarumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na sadarwar zamani na Tuwita inda ta sha alwashin cewa daga wannan Sallar tela ya dena mata yangar dinki dan kuwa zata bude shagon dinkin ta. Hasalima fitacciyar jarumar ta ce ita tuni an kammala yi mata dinkunanta.
Haka zalika jarumar tace ta shirya tsaf don bude shagon dinkin nata bayan sallah inda tuni ta tanadi teloli da duk wani abu da take bukata dan fara wannan sana'a.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng