Kololuwar cin amana: Wani matashi ya haikewa yarinya ƴar shekara bakwai da haihuwa
- Rashin imanin wani matashi da ya gaza kai zuciyar shi nesa ya janyo masa jangwam
- Yanzu haka kotu ta tisa keyar shi gidan yari sakamakon aika-aikar da yayi ga wata karamar yarinya
Wata kotun majistiri dake zamanta a Ikeja a birnin Legas ƙarƙashin mai shari'a Magistrate B.O. Osunsanmi, ta ingiza ƙeyar wani matashin ɗan kasuwa zuwa gidan kaso bisa tuhumarsa da ake da cin zarafin wata yarinya ƴar shekaru 7 da haihuwa.
Matashin mai suna Moses Austine ya roki kotun da ta yi masa afuwa amma alkalin ya ki amincewa da bukatarsa inda ya bukaci da a cigaba da tsare sa a gidan yari na Kirikir.
Jami'in ɗan sanda mai gabatar da ƙara Ezekiel Ayorinde ya shaidawa kotun cewa, matashin ya aikata wannan taɓargaza ne a gidansa a unguwar Atire dake jihar ta Legas a ranar 1 ga watan Yunin da muke ciki.
Ya bayyanawa kotu cewar matashin ya ketawa yarinyar haddinta ne bayan da ya gane cewa mahaifiyarta ta tafi aiki.
KU KARANTA: Harin ta’addanci: An kashe mutane biyu a Masallaci yayin da suke Sallar Asubah
"Ya kirawa yarinyar ne kamar yana son ya aiketa, bayan da yarinyar ta shigo cikin dakinsa sai ya rufe ƙofa ya kuma danne ta tare da aikata mummunan aiki akanta".
"Bayan mahaifiyar yarinyar ta dawo daga aiki sai ta riske yarinyar cikin yanayi na kuka idan ta tambayeta abinda ya faru, ita kuma ta kwashe komai ta faɗa mata".
"Mahaifiyar bata wani bata lokaci ba wajen shigar da ƙara a ofishin yan sanda, inda nan take jami'an mu suka kamo wanda ake tuhuma da aikata lefin" A cewar Ayorinde.
Laifin da matashin ya aikata ya saɓawa kundin laifuka na jihar ta Legas ƙarƙashin sashi na 137 na kudin manyan laifuka na shekara ta 2015.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng