Wata kungiyar addinin musulunci ta ciyar da mutane sama da 15,000 a watan Ramadana

Wata kungiyar addinin musulunci ta ciyar da mutane sama da 15,000 a watan Ramadana

Wata kungiyar matasan musulmi mai suna Bodija Muslim Youth Forum ta ciyar da al'umman musulmi sama da 15,000 abincin iftar (bude baki) cikin shirye-shiryen azumin watan Ramadana da ta shirya a garin Ibadan babban birnin Jihar Oyo.

Ciyaman din kungiyar reshen matasa, Alhaji Abdur-Rahman Balogun ne ya bayar da wannan sanarwan a wata bude baki na musamman da suka shirya.

KU KARANTA: Yaki da Rashawa: Ingila za ta hana barayin gwamnatin Najeriya guduwa su buya a kasarta

Balogun ya ce sama da mutane 500 da ke zaune a Bodija da unguwanin da ke makwabtaka dashi ne ke amfana da abincin bude bakin a kullum tun farkon azumin watan Ramadan a ranar 17 ga watan Mayu.

Wata kungiyar addinin musulunci ta ciyar da mutane sama da 15,000 a watan Ramadana
Wata kungiyar addinin musulunci ta ciyar da mutane sama da 15,000 a watan Ramadana

Ya ce a karshen watan Ramadana da zai fado a ranar 29 ko 30 na watan, sama da mutane 15,000 ne suka amfana da ciyarwar da kungiyar keyi.

Balogun ya ce kungiyar ta cinma matsayar fara bayar da abincin Iftar din ne bayan ta lura cewa mutane da dama a garin Ibadan ba su da ikon ciyar da iyalansu abinci musamman a watan azumin.

Ya kuma ce yana daga cikin koyarwan addinin musulunci taimakawa wadanda basu da karfi a lokacin azumi da bayan azumin ma saboda lada da ke tattare da aikata hakan.

Sai dai Balogun ya ce yafi dace a ciyar a watan Ramadana fiye da sauran watanni saboda darajar da watan ke dashi.

"Muna shirya bude bakin ne saboda al'ummar musulmi da ke zaune a unguwar Bodija da kewaye duk da cewa wadanda ba musulmi ba sukan zo bude bakin tare da mu a kullum," inji shi.

A kan yadda kungiyar ke samo kudaden da ta ke gudanar da wannan ayyuka, Balogun ya ce wasu masu tausayin talakawa ne da kuma wasu kamfanoni masu zaman kansu ke taimakawa kungiyar.

Duk da hakan, Ciyaman din ya sake kira ga sauran al'umma masu hannu da shuni su taimakawa wa kungiyar saboda su samu ikon cigaba da aikin alkhairin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164