An kama matashi dan shekara 18 dake shigar mata yana damfarar maza

An kama matashi dan shekara 18 dake shigar mata yana damfarar maza

Rundunar yan sandan Minna, jihar Niger sun kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Shamsu Abubakar inda yake shiga irin ta mata yana damfarar maza.

An kama shi ne sanye cikin hijabi da zani, inda ya sha kwaliyya sannan yasa takalmi da jaka iri guda na mata.

Shamsu wanda ke zama a yankin Sayako hanyar Maitumbi, Minna, ya bayyana cewa ya dauki tsawon watanni yana wannan sana’a sannan kuma yayi nasarar damfarar maza da dama.

Shamsu ya bayyana cewa yana siyar da sabulun wanke bandaki a unguwanni Minna tsawon watanni kafin ya koma wannan sabuwar kasuwanci, wanda a cewarsa yafi kawo kudi amma yana da hatsari.

An kama matashi dan shekara 18 dake shigar mata yana damfarar maza
An kama matashi dan shekara 18 dake shigar mata yana damfarar maza

Da yake Magana a yayin gurfanar da shi kakakin yan sandan Minna, ASP Muhammed Abubakar, yace yan sanda sun kama mai laifin ne bayan sun samu labarinsa.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 6 da ya kamata Musulmi ya sani kafin sallar Idi

Da aka nemi sanin dalilinsa na yin wannan shiga sai yace yana so ya dunga samun kudi ne daga mazan da zasu tsayar da shi su nuna suna son sa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wata kotun majistare na Osun dake zama a Modakeke, Ile-Ife ta gurfnar wani Emmanuel Ademakinwa mai shekaru 29 kan yunkurin yiwa mai ciki fyade.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel