Abubuwa 6 da ya kamata Musulmi ya sani kafin sallar Idi

Abubuwa 6 da ya kamata Musulmi ya sani kafin sallar Idi

Duk musulmin da ya yi azumin watan Ramadan, an so ya cika azumin da sallar Idi.

Al'umman Musulmi kan raya washen garin ranar kammala azumin Ramadana, inda akeyin gagarumin biki domin godiya ga Allah madaukakain sarki.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ya kamata mutum ya sani kafin wannan rana:

1. Fitar da zakkar fidda-kai ga marasa karfi

Zakatur fitr dole domin manzon Allah ya wajabta ta. Ta fi falala a fitar da ita kafin a tafi masallacin Idi.

2. Cin abinci kafin tafiya masallaci

Cin abinci kafin Idi koyarwar annabi ne. Ana so mutum ya ci abinci kafin zuwa Idi domin koyi da Manzo Allah.

3. Wankan zuwa Idi

Sunnah ce yin wanka kafin tafiya masallacin Idi. Ana son mutum ya yi wanka a ranar Idi kamar yadda yake wankan zuwa Juma'a.

4. Sanya kayamasu kyau

Kamar yadda muka sani Monzon tsirra ya sanar da Musulmi sabbin kaya masu kyau.Tufafi na musamman, kuma ga maza an fi son ya kasance tufafi farare.

5. Zikiri a lokacin tafiya masallacin Idi

Ana so mutum yayi ta kabbara a lokacin tafiyarsa Idi har idan an zauna a filin Idi zuwa sai liman ya zo.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa - Adesina

6. Chanja hanyar tafiya da dawowa daga masallacin Idi

Wannan koyarwar Annabi Muhammad SAW ba a son a bi da hanya daya. Ana son mutum ya chanja hanya idan zai dawo daga masallacin Idi.

A bangare guda Legit.ng ta rahoto cewa ana nan ana bukin sallah a kasar Nijar bayan bayyanar jinjirin wata a wasu biranen kasar.

A nan gida Najeriya kuma ana sanya rai gobe, Juma'a 15 ga watan Yuni za'ayi bikin karamar sallah kamar yadda kungiyar musulunci ta bukaci a fara neman wata a yau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Za ku iya samun mu a shafukanmu na:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel