A yau ne mutanen jumhuriyyar Nijar ke bikin Sallah
Mutanen Jamhuriyar Nijar, sun kammala azumin watan Ramadana, bayan an shaida ganin jaririn watan Shawwal cikin garuruwa da dama a kasar.
Da yammacin ranar Laraba, 13 ga watan Yuli ne al'ummar kasar suka kai azumi na 29, kuma a yau Alhamis, 14 ga watan Yuli suka wayi gari ranar karamar sallah inda za a fara bukukuwan sallar.
Rahotanni sun kawo cewa fira ministan kasar, Birji Rafini, na bayyana sanarwar ganin watan a ranar Larabar.
Mutane da dama sunyi korafin cewa sallar ta zo musu da ba dadi, saboda matsin tattalin arziki, da kuma ranar da aka kwalla a cikin watan azumin.
Mutanen kasar ta Nijar sun ce, da dama daga cikin al'ummar kasar ba su dinka kayan sallah ba, sai dai za su wanke tsoffin kayansu ne su je sallar idi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari zai sanya hannu a kasafin kudin 2018 a mako mai zuwa - Adesina
Al'ummar kasar ta Nijar dai sun ce anjima ba a shiga matsi na tattalin arziki ba a kasar, kamar wannan lokaci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Za ku iya bidar mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng