Labari mai dadi: Za’a fara kidayan adadin mutanen da jami’an Yansanda ke ci zarafinsu

Labari mai dadi: Za’a fara kidayan adadin mutanen da jami’an Yansanda ke ci zarafinsu

Babban sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris ya amince a fara bincikar ayyukan jami’an rundunar yansanda na musamman wato SARS don tabbatar da zargin tauye hakkokin biladama akansu ko kuma akasin haka, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

IG ya amince da wannan binciken kwakwaf ne bayan mika masa bukatar haka da hukumar kare hakkin dan adam ta kasa ta yi masa, inda tace tana bukatar ganin iya hakkin mutanen dake daure a hannun SARS.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Kotu ta kwace naira biliyan 2.2 daga wajen wani babba a gwamnatin Jonathan

A cikin wani rahoto da majiyar Legit.ng ta samu, hukumar kare hakkin biladama ta bukaci yan Najeriya dasu kai mata rahoton duk wani zargin cin zarafi da jami’an SARS suka yi musu, don bincikar lamarin.

Labari mai dadi: Za’a fara kidayan adadin mutanen da jami’an Yansanda ke ci zarafinsu
Jamian SARS

Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter, inda tace: “Babban sufetan Yansanda ya amince da bukatar hukumar kare hakkin biladama ta kasa, NHRC na duba dukkanin wuraren da Yansanda ke ajiye masu laifi, ciki har da na SARS.

“Wannan aiki zai baiwa NHRC damar gane iyakar cin zarafi tare da danne hakkin mutane da zargin Yansanda na yi ma mutanen da suke kame, don haka duk wani mai korafi ya bamu rahoto ta wadannan kafafen: Kira:0805 700 0001, 0805 700 0002, sakon kar ta kwana da WhatsApp: 0805 700 0003, BBM:58A2B5DE, Facebook: http://www.facebook.com/PolicePCRRU)facebook.com/PolicePCRRU.” Inji sanarwar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel