Rikicin Benuwe: Yan bindiga sun kai ma wani Janar na Soja harin kwantan bauna a gidansa

Rikicin Benuwe: Yan bindiga sun kai ma wani Janar na Soja harin kwantan bauna a gidansa

Gungun yan bindiga sun kai ma manjo janar John Malu hari a gidansa dake kauyen Tse Adoo a cikin karamar hukumar Katsina Alan a jihar Benuwe a ranar Litinin 11 ga watan Yuni, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Allah ya takaita barnar da za’ayi da zuwan Sojojin dake gadin Malu, inda suka dinga musayar wuta da yan bindigar har sai da suka ruga da kafarsu, sai dai Sojojin basu kama kowa ba.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Kotu ta kwace naira biliyan 2.2 daga wajen wani babba a gwamnatin Jonathan

Rahoranni sun tabbatar da cewar yan bindigan sun samu labarin zuwan Janar Malu ne, don haka suka mamaye shi suka dira gidan nasa, inda suka shiga harbin mai kan uwa da wabi, amma babu tabbacin ko wani ya jikkata sakamakon harbe haren.

Rikicin Benuwe: Yan bindiga sun kai ma wani Janar na Soja harin kwantan bauna a gidansa
Janar Malu

Babban kwamandan rundunar Sojoji ta 72 dake jibge a garin Makurdi,Laftanar kanal Suleiman Mohammed ya tabbatar da harin, inda yace: “Gaskiya ne wasu yan bindiga sun kai ma Janar hari a gidansa da misalin karfe 7 na safe, amma Sojojin dake gadinsa sun fatattakesu."

Daga karshe kwamanda Suleiman ya tabbatar da cewar Janar Malu na cikin gidan a lokacin da yan bindigar suka dira gidan, amma ya bayyana cewa babu abinda ya same shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel