Pasto Suleiman mai rigima da El-Rufai, na kuma rigima da mahaifinsa kan Buhari, leka kuji me yayi zafi

Pasto Suleiman mai rigima da El-Rufai, na kuma rigima da mahaifinsa kan Buhari, leka kuji me yayi zafi

- A baya, an sha jin kan PAstor Suleiman kan batun fulani makiyaya

- Ya taba alkawarin adduar da zata kashe Gwamna ElRufai kan dokar hana su wa'azi

- Yanzu kam dara taci gida

Pasto Suleiman mai rigima da El-Rufai, na kuma rigima da mahaifinsa kan Buhari, leka kuji me yayi zafi
Pasto Suleiman mai rigima da El-Rufai, na kuma rigima da mahaifinsa kan Buhari, leka kuji me yayi zafi

Hon Imoudu Sule, sannan miloniyan dankasuwa kuma shugaba a yada addinin kirista, Apostle Johnson Suleiman, shine shugaban jam'iyyar APC a Auchi kuma mataimakin shugaban jam'iyyar a Etsako ta yamma a jihar Edo.

A wata hirar sabon karta kwana da yayi da yan jaridu a Legas, shugaban ya bayyana dalilin da yasa sai fito yayi ma Dan shi jan kunne na karshe akan kalubalantar Gwamnatin Muhammadu Buhari da yake yi a koda yaushe.

A lokacin da yake bayyana tsananin kaunar da yake wa Dan shi, Suleiman Johnson, a lokaci guda kuma yake bashi shawara da ya maida hankali kan kira zuwa addinin kirista, Hon. Sule Imoudu yace ba zai saurara wa koma waye ba, da zai kalubalanci fada da rashawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa gaba.

"Wannan mutum ne da nake so, girmamawa kuma na bashi babban matsayi domin zaman shi mai nagarta"

DUBA WANNAN: Cikakkun bayanai kan yadda Dariye ya karke a kotu

Duk lokacin da naji jam'iyya ta, zuciya ta takan tsinke.

Apostle Suleiman dana ne amma ya zama Dan adawa ga jam'iyyar tawa. Kuma abun na damuna don masoya na tayin magana akan in kwabi dana.

A don haka ne nake magana, kowa yaji ni, naja kunnen shi da ya bar siyasa ga yan siyasa, ya maida hankali gurin zama shugaban addini.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng