Dakta Gumi jahili ne, yana bukatar ya koma makaranta - Sheikh Baban Tune

Dakta Gumi jahili ne, yana bukatar ya koma makaranta - Sheikh Baban Tune

Ana cigaba da yamutsa gashin baki akan maganganun da babban malamin nan na Musulunci, Sheikh Gumi yayi kwanan nan.

Shehin malamin dai ya soki al’amarin yaki da rashawar da gwamnatin shugabna kasa Muhammadu Buhari da hukumar EFCC ke yi.

Ya nuna cewar bai dace a tuhumi barayin gwamnati akan dukiyar kasa da suka sace ba.

Hakan ya sa Shugaban majalisar limamai da malamai ta jihar Kaduna sheikh Usman Abubakar Baban Tune yace wadannan kalamai sun nuna jahilcin shi a fili, kuma ya dace ya kusanci malamai domin neman ilimi.

Yayi wannan furuci a lokacin da yake jawabi yayin rufe karatun tafsirin karatun Al kur'ani na watan azumi wanda ya saba gabatarwa a babban masallachin juma'a na kamfanin matatar man fetur NNPC dake Kaduna.

Dakta Gumi jahili ne, yana bukatar ya koma makaranta - Sheikh Baban Tune
Dakta Gumi jahili ne, yana bukatar ya koma makaranta - Sheikh Baban Tune

Shehin Malamin ya cigaba da cewar, abin bakin ciki ne da takaici maganganun Dr Gumi inda yake bayyana kudin gwamnati a matsayin kudin banza kuma duk wanda yaci kudin yaci banza, inda yace wannan kalami ba karamin jahilci da ganganci Dr Gumi ya nuna ba kuma majalisar limamai da malamai tayi Allah wadai da su.

KU KARANTA KUMA: Kalli mai shari’a Adebukola Banjoko wacce ta yankewa tsoffin gwamnoni 2 masu ji da iko hukuncin zaman gidan kurkuku na shekara 28

Daga karshe Sheikh Baban tune ya bayyana goyon bayan majalisar su akan yaki da cin hanci da rashawa da EFCC ta keyi, inda yayi kiran hukumar data kara matsa kyami wajen zakulo barayin gwamnati da hukunta su, domin zama darasi ga 'yan baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng