Tsaffin gwamnoni 4 da aka taba turawa gidan yari a Najeriya
Duk da yadda kasar Najeriya tayi kaurin suna a ciki da wajen kasar game da matsalar cin hanci da rashawa, tabbas kasar ta samu nasarori da dama musamman ma a kan yakin da take yi da masu yi wa tattalin arzikin zagon kasa.
Ba kasafai ne ba dai kotuna a Najeriyar suke tsayawa kai-da-fata su yi shari'ar gaskiya tsakani da Allah musamman ma akan mutanen da ake ganin manyan masu kudi ne ko kuma mulki a da.
KU KARANTA: PDP tayi karin haske game da dan takarar ta a zaben 2019
Ko da yake a da din ba'a cika samun shari'ar adalci ba a cikin kasar, a kasar waje wasu 'yan Najeriyar da dama sun sha gamuwa da hushin hukuma akan laifukan da suka aikata na cin hancin da rashawa.
Sai dai a 'yan shekarun nan musamman ma tun bayan hawan wannan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari, an dai samu cigaba sosai da har wasu tsaffin gwamnoni biyu suka samu hukuncin zaman gidan yari.
Legit.ng dai ta tattaro mana wasu daga cikin tsaffin gwamnoni a Najeriya da aka taba garkamewa bisa laifin wawure dukiyar al'umma a kwana-kwanan na a wannan jamhuriyar:
1. Diepreye Alamieyeiseigha - tsohon gwamnan jihar Bayelsa
2. James Ibari - tsohon gawamnan jihar Delta
3. Jolly Nyame - tsohon gwamnan jihar Taraba
4. Joshua Dariye - Tsohon gwamnan jihar Filato
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng