Karfin fitar da mai ya ragu a wannan watan, hakan na nufin lalitar gwamnati zata yi kasa

Karfin fitar da mai ya ragu a wannan watan, hakan na nufin lalitar gwamnati zata yi kasa

- Tsarin fitar da man ya hada da cargo 48,Idan aka kimanta da cargo 60 da kuma miliyan 1.796 a watan yuni

- Tsarin fitar da man na watan yuni ya hada da cargo hudu na Akpo da 123,000 a rana, Idan aka danganta shi da cargo hudu a yuni na 133,000 a duk rana

- Tsarin ya nuna karin cargo daya na Agbami fiye da na watan yuni, tare da karin Bona daya da Qua Iboe

Karfin fitar da mai ya ragu a wannan watan, hakan na nufin lalitar gwamnati zata yi kasa
Karfin fitar da mai ya ragu a wannan watan, hakan na nufin lalitar gwamnati zata yi kasa

Akwai alamun cewa fitar da mai a Najeriya zai fadi a watan yuli zuwa ganga miliyan 1.43 a kowace rana, haka alamun suka nuna, mafi karanci a wannan shekarar.

Wannan zai zo ne a lokacin da Morocco da Najeriya suka sa hannun hadin guiwa a Rabat, don fara abu na gaba domin kammalar zancen bututun gas da zasu gida a teku da tudu.

Tsarin fitar da man ya hada da cargo 48,Idan aka kimanta da cargo 60 da kuma miliyan 1.796 a watan yuni.

Tsarin fitar da man na watan yuni ya hada da cargo hudu na Akpo da 123,000 a rana, Idan aka danganta shi da cargo hudu a yuni na 133,000 a duk rana.

Tsarin ya nuna karin cargo daya na Agbami fiye da na watan yuni, tare da karin Bona daya da Qua Iboe.

Ya nuna raguwar Forcados uku da kuma Escravos daya.

DUBA WANNAN: Zamu bar APC - Nyako

Tsarin fitar da mai a Najeriya ya saba da bita da bata lokaci, da kuma cargo da ake turawa daga wata zuwa wata.

Kasashen biyu sun amince da gida bututun a watan Disamba 2016 da kuma kaddamar da duba yuwuwar hakan, inda suka ka yanke shawarar gida shi a teku da tudu, sun ce :

"Saboda dalilan tattalin arziki, siyasa, shari'a da kuma tsaro, mun zabi gina bututun a teku da tudu"

National office of Hydrocarbons and mines da kuma matatar man fetur ta Najeriya zasu duba aikin, suka ce : "Bututun zai yi tsawon kilometers 5,660."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel