Cikakkun bayanai kan dalilan da suka sa aka yanke wa Joshua Dariye shekaru 14 a gidan Jarun

Cikakkun bayanai kan dalilan da suka sa aka yanke wa Joshua Dariye shekaru 14 a gidan Jarun

- An daure Dariye shekaru 14 a gidan kaso

- Ga alama wasu gwamnonin ma suna nan tafe

- Cikakkun bayanan yadda ta kaya har aka kai ga haka

Cikakkun bayanai kan dalilan da suka sa aka yanke wa Joshua Dariye shekaru14 a gidan Jarun
Cikakkun bayanai kan dalilan da suka sa aka yanke wa Joshua Dariye shekaru14 a gidan Jarun
Asali: Depositphotos

A ranar talata, mai shari'a Adebukola Banjoko ta karanto hukuncin ta daga laptop wanda ya kawo tsayawar iska cak. Sati biyu kacal da ta gabata, Mrs Banjoko ta yanke irin hukuncin a makamancin laifin.

A karshen wannan karar ta farko, tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ta yanke wa hukuncin shekaru 14 a gidan kaso sakamakon almubarrazantar da dukiyar jihar.

Da take karanto hukuncin ranar Talata,gungun yan jaridu, lauyoyi da sauran masu sauraron shari'ar a kotun Abuja sunyi mamakin ko abinda ya faru da Mista Nyame zai faru da Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar filato, wanda take karanto hukuncin shi.

Mista Dariye, Sanata mai wakiltar filato ta tsakiya, ana zargin shi da watanda da Naira 1.162 biliyan mallakin jihar.

Hukumar yaki da rashawa ta gurfanar dashi gaban kuliya a 2007.

Zaman kotun wanda ya dauka tsawon shekara 8,ya cigaba ne bayan da kotun koli ta umarci da aci gaba da sauraron karar a 2015.

An fara da ji daga bakin mai kare Mista Dariye, Kanu Agabi, yace akwai nakasu a karar saboda wasu dalilai. Daga baya kuma mai shari'a Adebukola Banjoko ta karanto laifukan kamar haka:

DUBA WANNAN: Borin kunyar Joshuwa Dariye

Bayan bincike da Peter Clark (Dan sanda mai bincike daga UK) ya gano wasu pam 816,000 a kasar waje mallakin Mista Dariye.

Bayan tsananin bincike, an gayyaci Mista Dariye don amsa wasu tambayoyi, inda aka bada belinshi da sharadin, ai koma UK don kara amsa wasu tambayoyi.

Bayan da yayi alkawarin zai koma, Mista Dariye yaki komawa.

A Najeriya, ana zargin shi da waskar da kudaden wasu kungiyoyin har da Jami'iyyar PDP.

Kudaden an tura su ne ga wani asusun mai suna Ebenezer Rethnam wanda daga baya bincike ya nuna Mista Dariye ne.

Daga baya aka samu wani shaida da ya tabbatar da har da Jami'iyyar PDP Mista Dariye ya turawa kudin, inda mai shaidar yace bai ga laifin shi ba saboda jam'iyyar shi ce ke mulki. Abinda ya zama abin mamaki da kuma kunya.

Mista Dariye bai taba tunanin yin bayani akan komai ba don kare kanshi daga watanda da dukiyar da ake zargin shi da ita.

A rashin wani takamaiman shaidar da zata wanke Mista Dariye, Mrs Banjoko ta kama Dariye da laifi 15 cikin 23 da ake zargin shi da su. Ta yanke mishi hukuncin shekaru 14 a gidan yari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng