Babu ruwan Buhari a hambarar da gwamnati na – Tosohon shugaban kasa Shagari
Tsohon zababben shugaban kasar Najeriya, Alahji Shehu Shagari, y ace shugaba Buhari bay a daga cikin sojojin da suka hambarar da gwamnatin sa.
Shagari ya bayyana cewar sai bayan da aka kifar gwamnatin sa ne ana neman mutum mai gaskiya da zai rike Najeriya daga cikin sojoji sannan aka ambaci Buhari.
“Ba Buhari ne ya yi min juyin mulkin ba, sunan Buhari bai shigo cikin juyin mulkin da aka yi min ba said a ake neman soja mai gaskiya da rikon amana da za a damkawa shugabancin Najeriya,” a cewar shagari.
Shagari ya kara da cewa, “Janar D. Y Bali ya kawo shawarar bawa Buhari mulkin Najeriya, kuma dukkan sojojin da suka yi min juyin mulki suka amince da shawarar sa. Tunde Idiagbon ne ya bayyanawa duniya cewar Buhari ne sabon shugaban kasar Najeriya duk da a lokacin yana can kasar Indiya inda yake halartar wani kwas.”
DUBA WANNAN: Kaico!: Ki taimake ni, nima fa kirista ne - Karanta yadda Dariye ya yi ruwan magiya ga alkaliya bayan yanke masa hukunci
An zabi Alhaji shehu Shagari a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 1979 a karkashin jam’iyyar NPN kafin daga bisani sojoji su yi masa juyin mulki bisa zargin gwamnatin sa da kama karya da cin hanci.
Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ne ya zama shugaban kasar Najeriya na mulkin soji bayan an hambarar da gwamnatin Shagari kafin daga bisani Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya yiwa Buhari juyin mulki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng