Gasar cin kofin Duniya: Hukumar kwallon kafa ta Arjantina ta yi abin kunya
Kungiyar kwallon kafar Arjentina na cigaba da atisaya a kasar Rasha a dadai lokacin da ya rage yan kwanaki kadan a fara gasar cin kofin duniya ta 2018.
'Yan wasan Arjantina sun fita fili don motsa jiki inda aka aikata abun kunya ga masu sha'awar kallonsu.
Hukumar Kula da Kwallon kafa ta Arjentina ce dai ta yanke hukuncin cewa, banda 'yan jaridar da suka je da su Rasha daga gida babu wanda zai shiga kallon 'yan wasan.
A bangare guda kuma, Kungiyar yan Super Eagles sun amshi babban lambar yabo a matsayin tawagar da kayan tafiyarsu yafi kayatarwa.
Sun samu wannan karramawa ne daga kamfanin British Broadcasting Corporation (BBC), a kasar Rasha yan kwanaki kadan kafin fara wasar ci kofin duniya na 2018.
KU KARANTA KUMA: Kalli hotunan 'yan wasan Super Eagles a yayinda suka isa kasar Rasha
Hakan na kunshe ne a cikin mujallar kwalliya ta duniya GQ inda aka kiyasta kayan kwallon yan Najeriya a matsayin wanda yafi kyau a na yan kwallon 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng