Wani Hatsari ya salwantar da Rayuwar Mutane 8 bayan dawowar su daga 'Kasar Andalus

Wani Hatsari ya salwantar da Rayuwar Mutane 8 bayan dawowar su daga 'Kasar Andalus

Mutane takwas ne da suka hadar da maza biyar da mata uku suka rasa rayukan su a wani mummuna hatsarin Mota da ya afku a safiyar yau ta Talata jim kadan bayan dawowar su daga Kasar Andalus watau Spain.

Wannan hatsari ya afku ne da misalin karfe 8.30 na safiyar yau kilomita 2 daura da Gidan Mai na Danco a babbar hanyar dake tsakanin Biranen Legas da na Ibadan.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, dukkanin wadanda hatsarin ya ritsa da su 'yan asalin jihar Edo ne da suka shigo Najeriya yayin dawowar su daga Kasar Spain a safiyar yau ta Talata.

Mutane 8 'Yan asalin Jihar Edo sun gamu da Ajali akan hanyarsu daga 'Kasar Andalus
Mutane 8 'Yan asalin Jihar Edo sun gamu da Ajali akan hanyarsu daga 'Kasar Andalus

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan hatsari ya salwantar rayukan mutane takwas yayin da suke kan hanyar su ta zuwa birnin Benin na jihar Edo domin halartar bikin baiko na wani dan uwa na su.

KARANTA KUMA: Kotu ta dakatar da Shari'a don ba Dariye damar Kewayawa Bayan Gida

Babatunde Akinbiyi, kakakin hukumar kula da manyan hanyoyi ta TRACE (Traffic Compliance and Enforcement Corps) reshen jihar Ogun ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a sakamakon tsala gudu da ya wuce misali da ka'idar tuki.

Legit.ng ta fahimci cewa, rayukan mutane bakwai ne suka salwanta yayin afkuwar hatsarin inda bayan garzayawa da su asibitin koyarwa na Olabisi Onabanjo dake birnin Shagamu cikon na takwas din su ya ce ga garin ku nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng