Bayan kashe abokinsa da yayi don tsafin yayi kudi, yana mamakin wai har yanzu yana cikin talauci

Bayan kashe abokinsa da yayi don tsafin yayi kudi, yana mamakin wai har yanzu yana cikin talauci

- Da yawa masu yarda da camfi kan dauka tsafi ko asiri gaskiya ne

- Wani matsafi ya kashe abokinsa don yayi kudi amma talaucin bai barshi ba

- Zahiran hanyar kudi ita ce kawai sa'a da iya nema

Bayan kashe abokinsa da yayi don tsafin yayi kudi, yana mamakin wai har yanzu yana cikin talauci
Bayan kashe abokinsa da yayi don tsafin yayi kudi, yana mamakin wai har yanzu yana cikin talauci

Wani mutumi mai suna Daniel mai matsakaicin shekaru wanda ya hada kai da wasu mutane biyu gurin kashewa da cire zuciyar wani abokin su, Isaiah James, don tsafi. Yace dana sanin shi daya, basu fara samun kudi ta hanyar tsafin ba kafin a kama su.

Kamar yanda Daniel yace, wanda aka kama a bangaren Ajah na jihar Legas kuma ake tuhumar shi a bangaren tuhumar yan ta'adda dake jihar a yankin Yaba tare da wasu mutane uku.

"Nayi dana sanin kashe abokina. Duk da banji komai ba da nake cire zuciyar shi. Kashe mutum dai dai yake da kashe dabba. Dana sanina shine bamu fara yin kudin ba kafin a kama mu."

Daniel yace "Daga Chibok nake ta jihar Borno. Audu, Ayuba da ni muka hada kai gurin kashe abokin mu, Isaiah James, saboda tsafi. Tun farko ba haka muka shirya ba. Munso ne muyi laya don shahara a damfarar kudi, wanda aka fi sani da 419,amma bokan da muka je gurin shi yace bazai mana layar damfarar ba.

Da muka tambaye shi dalili sai yace mana ai bamu da ilimi. Yace sai munyi ilimi zamu iya damfara. Sai muka tambaye ko akwai wata mafita, shine yace ya tausaya mana zai yi mana tsafi. Shine yace mu kawo mishi zuciyar mutum. Sai muka ce ya taimaka ya nemo mana sai mu biya. Bokan yace mu kawo 100,000, inda muka biya N60,000 da alkawarin zamu cika sauran."

DUBA WANNAN: A Najeriya aka i zubda ciki duk duniya

"Kwanaki kadan matsalar ta fara, lokacin da bokan ya kira mu yace yan banga sun harbi yaron da ya tura samo zuciyar a hannu. "

"Yace ba zai iya samo zuciyar ba, inda ya umarce mu da mu kawo da kanmu."

"Dabarar mu ta kare, sai daga baya Audu yace mana zai kira Dan uwanshi, wanda kuma abokin mu ne. Sai mu kashe shi, mu cire zuciyar. "

"Mun nemi da ya same mu a wata mashaya a Ajah, inda gurin karfe 1 na dare muka kama hanyar tafiya gida, a nan Audu ya fito da wuka, mu kuma muka dinga dukan shi, da muka ga ya kusa mutuwa, sai muka yanka shi muka fitar da zuciyar."

"Mun kaiwa bokan inda yayi mana faten wake da ita, muka cinye. Yace daga yanzu komai muka sa hannu a kai sai yayi albarka. Mun cika mishi kudin shi zamu wuce kenan yan sandan suka kama mu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng